KALAMAN SOYAYYA GUDA ASHIRIN 20 MASU DADI
1. Indai muna tare da juna, Zamu rayu cikin aminci kasancewarki acikin Rayuwa ta ribace babba kuma wacce bata qarewa Ina sonki Sosai.
2. Ina farin ciki dake, kuma kina sani Farin ciki, kin chanja min rayuwa dole na fadawa duniya ke nake so Na sadaukar miki da rayuwata.
3. Bazan Iya Fadan Lokacin Da na fada Soyayya dake ba amma daga lokacin dana fara ganin ki nasan ke tawa ce, Ina Sonki.
4. Soyayya Na girma a kowace rana, Ke kika koyamin yadda zan gudanar da rayuwata, Soyayyar ki kamar haske take a samaniya idan kika fito kowa sai ya kalla, Ina Sonki.
5. Ganin ki yana Tabani a Zuciya, Haka Rashin ki Yana Tabamin Zuciya, ke wata kyauta ce da Allah ya Bani acikin duniyar nan. Ina sonki!
6. Idan na kalli cikin idanuwan ki akoda yaushe rikicewa nake, Hasken ki yana sa naji inada sauran rayuwa, ina son ki sani babu abunda zai Fansheki awurina. Domin kin riƙe zuciyata.
7. Akoda yaushe, a cikin ko wani hali, kece mai sani nishadi da farin ciki ina sonki sosai har Zuciya ta shiyasa bazan iya wuni guda ba tare dake ba.
8. Baki taɓa rabuwa dani ba, baki taɓa gajiya dani ba Motsina, Murmushi na, Kuka Na, Muhimmanci na, Koda Yaushe kina tare dani, kina kula dani, ina sonki sosai!
9. Naga Haske a idanuwan ki, Yana haskawa tamkar taurarin dake samaniya yana haskamin haryar zuwa gareki, Ina sonki.
10. Kin san me kika mini Kinsan me kika fada mini kin gigice saboda ni! Ko Yaushe Ina mamakin taya haka ta faru, inason ki sani kece mafi girman kyautar dana taɓa samu.
11. Kin fadi abunda nake son ki fada, kinyi abunda nake son kiyi, bansan taya kika aikata ba amma ya burge ni, nagode da kika kasance cikin rayuwata.
12. Kin bani dalilin kasancewa a raye lokacin da nake cikin kadaici Har yanzu kina sani sa rai anan gaba kina nunamin bazan Rayu idan bake ba, me zan nema idan ba ke ba? Zuciyata Mallakin ki ce!
13. Kalaman ki da Dabi’un ki sun chanja ni, Naji dadi ke tawa ce ni naki ne, wannan shaukin ne yake sakani farin ciki Sahibata kece Rayuwata!
14. Bazan manta dake ba, nayi rashin ki a baya amma yanxu gani kusa dake, zuciyar mu ta zamo daya.
15. Ina Taskake Duk wani lokacin da muke tare, domin shine abun tinawata a Kullum, na ajiyesu kusa da zuciyata, Bazan taba mantawa dake ba.
16. Kin nuna min asalin ma’anar Qauna, yadda take Da yadda ake jin ta. Ina Sonki!
17. Ranar dana Fara Ganin Ki, Zanen fuskar ki ta ya manne acikin zuciyata Ranar da kika Fadamin, kina so na, Sunan ki Ya zamo dashe a zuciyata.
18. Bana Tsammanin zan taba iya fadawa Soyayya da wata, kamar yadda na fada Soyayya dake ba Bansan me nayi na Cancance ki ba, amma na tabbatar Zan
Bi dake ta hanya mai kyau, You are mine!
19. Nasan Ban Chanchanchi Soyayyar ki ba, amma kina sona, ban kamaci samun kulawarki ba, amma Yau gaki kusa dani kina kulawa dani, Ke Kyauta ce daga Allah Nagode Abisa duk wata karrawa da kika nuna min.
20. Ana Cewa Ba’a samun abunda ake so, Amma ina jin dadi ina sonki kuma na sameki yanxu, Soyayyar ki agareni ta wuce darajar Zinare.
Agajahub publishers