KALAMAN SOYAYYA GUDA GOMA MASU GAMSAR DA RUHI

 KALAMAN SOYAYYA GUDA GOMA MASU GAMSAR DA RUHI

(1)-da akwai miliyoyin furanni acikin lambun masoya a wannan duniya, da a ce zan tsunko kowanne fure na baki shi a hannunki, hakan Bai Isa ya bayyanar da adadin yadda nake son ki ba, kece Murmushi na, kuma kece farin ciki na, Ina sonki.

(2)-sama cike take Da taurari masu hasken da ke haske duniya acikin kowanne dare, amma haske mafi haskaka fuska da yaye duhun zuciya, na gani shine a cikin idanuwanki, ki kula min da kanki, Ina sonki.

(3)-na daɗe ina kallon taurarin samaniya yayinda naga wacce tafi kowacce haske, saina naga bakowa bace nike ganiba sai ke masoyiyata.

(4)-so gamon jini ne, haqiqa sonki ya zamo jinin jikina.

(5)-kinfita daban a cikin Mata duk lokacin dana kalleki sai naga kamar babu kyakkyawar mace sai ke.

(6)-ki Kwantar da hankalinki masoyiyata babu wata a zuciyata saike kaɗai.

(7)-farin ciki baya ɗorewa a rayuwa sai tare da bakin ciki, Dan haka kowane hali nake Bazan taɓa mantawa dake ba masoyiyata.

(8)-kin fi dukkan Mata iya ado da iya tafiya, ina maraba da ke a cikin rawuyata, ina maraba da kasancewarki Mata a gareni, ina lale marhabun da kusantuwarki gareni.

(9)-yake masoyiyata ina mai daɗa tunatar dake irin matsayi da martaba da kike da ita a cikin zuciyata wanda a tarihin rawuyata ban taɓa son wata ‘ya mace ba wadda kullum so yake karuwa ba face ke.

(10)-a dukkan lokacin da tinaninki ya bijiromin a cikin zuciyata, na kan tina irin yadda sonki ya zamo Abu mai matuƙar muhimmanci a rayuwata, kece wadda nake so kuma nake fatar na rayu tare da ita, rayuwa ta har abada, Ina sonki.

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top