Kalaman soyayya masu dadi da kuma Kwantar da hankali tsakanin masoya.

Kalaman soyayya masu dadi da kuma Kwantar da hankali tsakanin masoya.

Assalamu alaikum masoyiyata 
Kyakkyawar fuskarki Na bayyanar da murmushi mai taushi da tausasa zuciyar ma,abucin kallonta, kece wadda nikeso acikin zuciyata.
Kada ki fadawa kowa kalaman sirrin bude soyayya da kawancen dake tsakanin mu, domin kuwa aduk lokacin da kika  furta wadannan kalaman sirri  ga wani wato “inasonka” hakan Na nuna cewa zaiyi amfani dashi wajan bude mana akwatin soyayyar mu ta sirri Wanda hakan zai bashi damar yi muna gagarumar sata har yayi sanadiyar ra bani da ke har abada “Ina son Ki”.

Danqon soyayya

Akullun nakan tambayi kaina cewa  wai shin akwai wata tamkarki acikin wannan nahiyar?

Haqiqa Ke kyakkyawace ta gaban kwatance wacce zan iya cewa babu tamkarki acikin wannan duniya gaki Fara mai dogon hanci tamkar karas murmushinki tamkar jaririn fure acikin furannan duniya sautin muryarki tamkar sarewar algaita ta sarakunan duniya daga karshe abinda zance shine “Ina son Ki”.
Ku ci gaba da bibiyar shafin mu agajahub domin kawo muku Da dadan kalaman soyayya da sauran sure.
Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top