KALAMAN SOYAYYA MASU DADI

KALAMAN SOYAYYA MASU DADI

Na Maza

-Ina neman wata kalma wadda babu wanda ya santa. Ina
neman wata kalma da zan furta miki
 cewa…..ke ta daban
ce, ke kyakkyawa ce, kin zarce sauran mata. Zuciya ta da
taki ba za su ta6a rabuwa ba har abada. Ina son ki.
-SO shi ne abun da ya dun’kule zuciyoyinmu waje guda har
muka tsinci kanmu a cikin soyayya, ina fatan ba za ki bari
wani d’an ‘karamin abu ya zo ya raba tsakaninmu ba? Ina
son ki. Ke tamkar gishiri ce a cikin rayuwa ta, idan na rasa
ki zan yi rayuwa ne da babu armashi a cikinta. Ki Huta
Lafiya.
-Da akwai wasu tarin tsintsaye da suke wuni suna tattauna
batutuwa a kan irin matsayin da na baki a cikin zuciya ta.
Zan so ki ji irin abun da suke cewa, domin kuwa a lokacin
ne za ki tabbatar da irin son da nake yi miki. Ina Son Ki!
-A lokacin da na samu soyayyarki sai na ji tamkar ni ne na fi
kowa sa’a a duniya. A dukkan sanda na rintse idanuwa na
sai na hango ni tare da ke muna tafiya a bisa gajimare. Idan
na kwanta bacci sai na yi mafarkin mun zama mata da miji.
Ina sonki, tare da son kasancewa a tare da ke har abada. Ki
Huta Lafiya.
-A dukkan lokacin da dare ya yi, ki d’aga kanki sama ki kalli
sararin samaniya, za ki ga wani tauraro yana saukowa izuwa
gare ki, karda ki yi mamakin me ya sa haka ya faru? Ki
yarda da ni, hakan zai iya faruwa a zahiri domin kuwa ni ma
na yi hakan har ta kai ga na same ki. Hmm! Ki Huta Lafiya
-sonki yana cikin zuciyata, amma ina kokwanton kada ya
zama tsuntsu ya tashi, idan har ma ya kasance kin ci gaba
da nuna rashin kulawarki a kaina
kyakkyawa mai kyan tsari,a duk lokacin da nake kallonki,
tamkar kyakkywar fulawa mai furanni ma’abota debe kewa
da sanya nishadi a zuciya ki kan zamo min
-A mafarki da kuma a cikin soyayya babu abun da ba zai iya
faruwa ba. Ina son ki sosai hakan ya sa nake ji tamkar ba
zan iya rayuwa idan ba tare da ke ba. Ba na fatan rasa ki a
rayuwa ta, domin kuwa a dukkan lokacin da na rasa ki, na
tabbatar da rayuwa ta za ta shiga garari. Ina Son Ki kuma ba
zan ta6a canjawa a kan hakan ba.

Na mata

-Tsuntsaye na bu’katar fukafukai domin tashi, kifi na bu’katar
ruwa domin ya yi rayuwa, ni kuma ina bu’katarka domin na
yi rayuwar farin-ciki. Ina son ka masoyi na!
-Ina son jinka a kusa da ni, ta yadda numfashi na da naka
zasu gauraya, ta yadda zan ke juyo sautin bugun
zuciyoyinmu na fita a tare. Mu kasance a tare har abada.
Ina Son Ka!
-Ina Son Ka, zan kuma ci-gaba da sonka tun daga fitowar
rana har izuwa faduwarta a cikin kowace rana har abada.
Ka Huta Lafiya
-A kullum na kwanta bacci, na kan yi mafarkin ka zama uban
‘ya’ya na, ni kuma na zama mata a gare ka. Sai dai na san
iya mafarki ba zai wadatar da ni ba a bisa kulawar da nake
tinanin samu daga wajenka. A saboda haka nake fatan
mafarki na ya zama gaskiya watarana. Ina Son Ka!
Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top