KALAMAN SOYAYYA MASU INGANCI GA MASOYA

KALAMAN SOYAYYA MASU INGANCI GA MASOYA

-Soyayyata a gare ki gaskiya ce, kuma ta ginu ne daga ranar da na fara ganinki, ina kaunarki fiye da yadda zan fada maki.
-Ina son yadda ki ke so na, kada ki yasar da ni, kada ki taba juya min baya, Ina sonki. Surely, I realy love you, and I want be your Husband forever, be with me please.
-Tabbas ina matukar ƙaunarki, kuma ina son kasancewa miji a gare ki har abada, don Allah ki kasance tare da ni. 
-Masoyiya ta a duk lokacin da naji muryar ki nakan samu natsuwa a zuciya ta,Murmushin ki a gare ni yafi aban kyautar duniya, Fiskar ki a kullum haske take kara yi musamman idan kina murmushi, Idan kikai fushi sannan ne kike daɗa kara kyan gani. 

-Amincin Allah ya tabbata a gareki masoyiyata, hasken idaniyar ki kanyi farin ciki matukar ina tare ke, na kan manta da dukkan wani damuwar da nake ciki idan ina tare dake, barka da safiya Nabaki rayuwa ta yadda kema kika bani rayuwarki Sautin muryar ki yana sanya ya mini raina, mu kwana lafiya.
-Kece abu na farko da nake tunawa lokacin da na tashi daga barci, tunaninki kawai mafi girman gurbi a fuskana.
-Akan kauna na manta kai na masoyiyata na ke tunawa SO shi ne abun da ya dunkule zuciyoyinmu waje guda har muka tsinci kanmu a cikin soyayya, ina fatan ba za ki bari wani ɗan karamin abu ya zo ya raba tsakaninmu ba.
-Ina son ki, Nakan ji mafi girman dadi a duniya a duk lokacin kika min sannu, ko kika min murshi, Ina kira ki.
-so wani abu ne mai kyawu, kuma wani yanayi ne da mutum zai so ya damke. So shi ne yanayin da kan sa ka ji ka a raye. Ina sonki.
-Ina fatan kin fahimci cewa zan so ki har karshe, saboda ba kin kasance budurwata kadai ba, ke ce Aminiyata. 
-Abu ɗaya da bazaitaba karewa ba ‘shi ne soyayyarmu da ke, saboda ke kadai ce a cikin zuciyata. 
-Duk sarakunan mata dake mulkin zuciyoyin masoya babu wata zuciya da ta kai tawa samun sarauniya mai adalci kamar ki, kece ruhina, kin zamto farin cikin raina.
-A kullum bani da burin sauraren wani zance in ba naki ba, ki Yiwa kowa fatan alheri koda akwai masu yimiki fatan sharri, saka dukkanin musulmi acikin addu’arki koda babu mai sakaki acikin addu’arsa,ki
Nufi kowa da alheri koda akwai masu nufinki da sharri.ki kyautata tsakaninki da Allah kada ki damu da abinda mutane suke cewa akanki. Allah ya kyautata rayuwarmu Amin, Ina sonki.
-MASOYIYATA  Kece wadda kika dace da sarautar zuciya ta don haka na baki ita kyauta, ki rikemin ita amana, Ina sonki har abada.
-Zan iya aiwatar da komai har idan ina jin kalaman ki masu sanyaya zuciya, Na yarda da ke na aminta da ke don haka na mallaka miki kaina Ina fatan zaki ci gaba da kula min da kan ki har zuwa lokacin da zan dawo gida Allah ya tsare min ke matata.
Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top