KALAMAN SOYAYYA MASU KARA DANKON SOYAYYA GA MASOYA!!
Na dade ina kallon taurarin samaniya yayinda
naga wacce tafi kowacce haske, saina naga
bakowa bace nike ganiba sai ke masoyiyata!
So gamon jinine, haqiqa sonki ya zamo jinin
jikina!
Kinfita daban a cikin mata, duk lokacin da na
kallleki, sai naga kamar babu kyakykyawar wace
sai ke!
Ki kwantar da hankalinki masoyiyata babu
wata a zuciyata sai ke kadai!
Yarda da amincewarki gareni, sune zasu
tabbatar da soyayyarki tagaskiya a gareni!
Farin ciki baya dorewa a rayuwa sai tare da
bakin ciki, dan haka kowane hali nike bazan ta6a
mantawa dake ba masoyiyata!
Nakan raba dare ina mai roqon Allah don
neman biyan buqata, ko kinsan kece abu na farko
da nike roqo samu!
Yanayin sanyi kan sa mutum ya takura, tare
da lullu6a da qaton mayafi amma ni duk sanyin da
ake idan na tunaki sai naji tamkar yanayin zafi!
Kamar yadda kowacce bishiya kanyi rassa a
sama, kuma tayi saiwa a qasa, haka sonki ya
mamaye dukkan jikina, idan na kalleki sai nayi
farin ciki, idan naji tattausan muryarki, sai nishadi
da walwala tare da annashuwa gami da farin ciki
su mamaye zuciyata!
Abun da na ke ji a dangane da ke gaskiya ne
kema na san kin san da haka cewa ina son ki, a
duk lokacin da kika bar ni ba zan iya motsawa ko
da nan da can ba, wannan shi ne abun da zai
faru da ni a duk lokacin da na rasa ki.
SO tamkar wata sarkar zinari ce da ta d’aure
zuciyoyin mu a waje guda, a dukkan lokacin da
kika tsinka waccan sarka tofa ki tabbatar da
cewa tamkar kin kore farin ciki ne daga cikin
zuciya ta.
ina son ka, me ya sanya ka ke yin
kokwanto a bisa kalmar so da na furta a gare ka?
Tabbas kaine mutum na farko da haduwa da shi
ya kore min bakin ciki, ya wanzar da farin ciki a
zuciya ta ya yalwata murmushi a saman fuska ta
hakane dalilin da ya sanya na ke kiran ka da
SADAUKI. Salim, ka yi nasara ka yi nasarar jan
ra’ayin soyayya ta a kan ka kaine na mallakawa
linzamin zuciyata, kaine mutum na farko da na
taba furtawa kalmar SO kuma a yanzuma zan
GAREKI SARAUNIYAR zuciyata isyama
❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
Soyayyarki itace babbar kyauta Dana taba samu a rayuwata ,zan killa ceki a cikin zuciyata na har abada , Idanuwana basuda da wani buri Wanda ya wuce suga kyakyawar fuskarki ,kunnuwa na basuda wani buri wand ya wuce suji zazzakar muryarki .haka zalika bakina bashida wani buri Wanda ya wuce in furta miki kalaman soyayya wadanda zasu sanyaya zuciyark Ga zuciyata nan ki dauka sannan ki kulamin da ita ,zuciyata cike take da soyayyar ki da kuma gaskiya , kada ki sata cikin kunci ki kasance mai sata farin ciki da annashuwa
,sonki akoda yaushe karuwa yake acikin zuciyata . Ina sonki da fatan kin wayi gari lafiya