KALAMAN SOYAYYA MASU KARA DANKON SOYAYYA GA MASOYA

KALAMAN SOYAYYA MASU KARA DANKON SOYAYYA GA MASOYA

-abindazuciya take so ta samu awurinki wannan yasa da Na zauna ina tunanin ki kawai na ga hawaye Na zuba daga cikin idona.

  -Furanni na furta kalmomin yabo a kanki a dukkan lokacin da na shiga lambu mai ɗauke da ƙorama gami da ƙorayen ciyayi da bishiyu masu d’auke da tsintsaye, Sukan rera baitukan yabo a gare ki, cikin harshen da zuciya ce kawai ke iya fahimtarsa. Ina Son Ki.

  -Amafarki da kuma a cikin soyayya babu abun da ba zai iya faruwa ba Ina son ki sosai hakan ya sa nake ji tamkar ba zan iya rayuwa idan ba tare da ke ba, Ba na fatan rasa ki a rayuwa ta, domin kuwa a dukkan lokacin da na rasa ki, na tabbatar da rayuwa ta za ta shiga garari. Ina Son Ki kuma ba zan taɓa canjawa a kan hakan ba.

 -Nakasance ma’abocin soyayya zuciyata ma ta gasgata hakan, Lokaci na shudewa soyayyarki na karuwa a cikin zuciyata.

 -Alokacin da ki ke cikin farin ciki kyakkyawar fuskar ki na bayyanar da murmushi mai taushi da tausa sa zuciyar ma’abocin kallonta, kece wadda na ke so a cikin zuciyata babu wata da za ta iya canja matsayin ki a wajena.

 -Sonki na haskawa a cikin zuciyata tamkar yadda tauraruwa ke haske a bisan sama. Ina sonki fiye da yadda kalmomi za su kwatanta hakan a rubuce.

 -Kinzamo ta musamman daga cikin mutane na musamman da na taɓa haɗuwa da su a rayuwata, kin shiga zuciyata kin zauna ta yadda ba zan iya mantawa da ke ba har abada, Ina fata da burin kasancewar mu tare a daula mafi tsari da kyawun burgewa wato Aljanna, Cikin nishaɗi da yalwatuwar murmushin fuska nake mai furta miki cewa Barka Da Safiya.

 -Shinwani ya taba sanar da ke cewa murmushin ki abin so ne? Sannan kuma a duk lokacin da kike yin murmushi ya kan mayar da fuskar ki tamkar wata fitila mai haske, Ke kyakkyawa ce, hakan ya sanya kwakwalwata ta zana mini kyakkyawar fuskar ki a cikin zuciyata wadda ta zamo abar nazarta a gare ni a duk lokacin da nake zaune ni ɗaya cikin kaɗaici a dare ko safiya, Ke ce abar so na.

 -Zankasance cikin baki furen soyayya a dukkan lokacin da muka haɗu, matuƙar na samu tukuicin murmushinki a kan haka, to fa tilas na gina mana gida cikin da’irar lambu mai cike da tarin furanni masu kyawun launi da daɗin ‘kamshi. 

-Inason dukkan taurarin da suke bisan sama, amma ba za’a haɗa son da na ke yi musu da kuma na wadda ta ke a cikin idanuwan ki ba, ina son ki.

 -Lokaci yana nan zuwa da zaki mallakawa wani zuciyar ki, ina mai yin kira a gare ki da ki tabbatar da cewa kin mallakawa wanda ba zai raunata zuciyar ki ta hanyar yaudara ko cin amana ba, saboda ita zuciya ɗayace babu wadda zaki dauko ki sauya a lokacin da bakin ciki da damuwa suka mamaye zuciyar ta ki.

 -Yanzu haka ina cikin farin ciki, shin kin kuwa san mene ne dalili? Hmm saboda na kasance mai sa’a, kin kuwa san tayaya, Saboda Allah ya na so na, kin kuwa san me ya sanya na ce haka?  Saboda ya ba ni wata babbar kyauta, kin kuwa san mene ne? Ba komai ba ne ba face KE masoyiyata, ina son ki.

 -Akoda yaushe lokaci tashi yake yi tamkar tsuntsu, amma ita soyayyar mu kullum ginuwa ta ke tare da kara samun wajen zama a cikin zuciyoyin mu karda ki manta da ni ki kasance mai yin tinani na kamar yadda nima na kasance a ko da yaushe.

-Sonki kamar numfashine a gareni, taya zan dai na.

-Nisa tsakanin zukata biyu baya nufi shinge face yana tuna mana da kyakyawar alakar dake tsakanin mu, Ina kewar Ki Mata ta uwar ‘ya’ya na.

-Nakan yi kewarki sosai a dukkan lokacin da na duba gefe na ban gan ki ba. kamar kullum, yanzu haka ina zaune cikin tinaninki.

-Zuciyata na cike da kewarki, zan samu sassauci ne kawai idan na ji ki a kusa da ni, Ki kula min da kanki har zuwa lokacin da zan dawo kulawarki ta dawo hannu na, Ina Son Ki.

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top