KALAMAN SOYAYYA MASU RATSA JIKI
Amincin Allah ya tabbata a gare ki ya ke wacce ta fi tauraroda duk wani haske. Haske a idanuwa na, Ina fatandai ba fushi kike da ni ba. Zan iya manta komai ammaka sani ba zan iya mantaka ba haka kuma zan iyajure rashin komai amma ba zan iya jure rashinka,ba hakika daga jiya zuwa yau ina cikin kunci mara misaltuwa bakin ciki ya ziyarci zuciya ta wanda har kawoi-yanzu ba na jin zan iya kula wani cikin walwala. Idanhar na ce zan iya na yi karya domin ni kadai na sanirin halin da nake ciki na rashin jin dadin tafiyarka.
Zuciyata na tafasa har nakan ji tamkar na fashe da kuka ka sani cewa wannan sakon zuciyata na sanar da kai hannu aikinsa rubutawa ba wai ina fada ne don tsari ko don ka ji dadi ba.
Daga lokacin da ka hada inaka-inaka ka yi gaba ni ma daga wannan lokacin na tattara duk wani walwala na da farin cikina na ajiye su a can gefe barin da ba zasu taba kusanto ni ba. Don haka ina sanar da kai banyi fushi da abin da ka aikata ba kuma ban kiraka donka bar abin da kake ba, illah na kira ka naji laifin ba daga gare ni yake ba. Ka kasance cikin farin ciki ka huta lafiya. Na gode da kulawa, amma ina ga ba ki kai nishiga kewa da zullumi ba, dama an ce ba a sanin muhimmancin mutum sosai sai alokacin da ya yi nisa dakai.Hakika jiya na kara gasgata wannan maganar.
Kalaman soyayya
Domin nisanta da na yi da ke na yini daya sai naji kamar shekaru dubu ne, Kin riga kin zama fatar jikina duk wanda ya raba ni da ke kamar ya raba ni da kyauna kwarjinina hade da suturata. Ke garkuwa ce a gare ni maikare ni daga abubuwa da dama, Hasken zuciyata farin cikin raina, annashuwa da jin dadi na. Ina sonki ina kaunar ki, ba zan iya nisa da ke ba. Ba zan barki ba duk rintsi duk wuya, Sai dai in ke kika bar ni zuciya kuwaba ta fatan ko mafarkin hakan balle a gaske. Ina soki sani cewa soyayyarki ta yi nisa cikin zuciyata. Ahankali – a hankali ina ta ba ki filayen zuciyata ina so in rasa kaina a garin yin hakan ta yadda ba zan taba samuwa ba da sannu sannu dai ina ta mika rayuwata izuwa gareki ya masoyiyata kinzama abar kaunata wannan duk saboda karamcin kine a gare ni a yayin da nake kara kusan tuwa dake duk tunane-tunane na suka fara bayyana ya masoyiyata kin zama abar kaunata kamar giza-gizai haka kika zamo inuwa a gare ni kamar ruwan sama haka kika jike ni da farin ciki kamar iska hakakika tafi da tunani na kin sabunta kaddarata ta hanyarsamar da sabuwar safiya a rayuwata.