KALAMAN SOYAYYA MASU RATSA JIKI

KALAMAN SOYAYYA MASU RATSA JIKI

 -kinwadata zuciyata da farin ciki, kin haskaka rayuwata da haskenki, kulawarki a gareni ta musamman ce, hakan yasa nake jin kaina tamkar sarkin wata masarauta mafi girma da karfin iko, Ina son Ki.

-kece kaddarar da najima ina tsimayin tarar da ita a rayuwata, zan kasance a duk inda kika tsayar dani, ina sonki adadin son da kalmomi ba zasu iya siffantuwa ba.

-koda ace zakisa wuta ajikina na babbake na zama toka, Bazan damu ba matuƙar zaki ɗauke ni, ki kasance tare dani aduk inda kike, fatana mu kasance tare da juna a cikin wuya ko daɗi, Ina sonki.

-son da nake miki tamkar ruwan lemu ne dake rufe acikin kwalba, irin wanda babu irin sa ko makamancinsa a fadin wannan duniyar, ina fatar zaki É—auka domin jin irin É—anÉ—anon dake kunshe a cikin sa, Ina sonki.

-ina fatar Allah ya barmu tare cikin aminci da ƙaunar juna.

-so tamkar wutar murhu ne dake ci a cikin zuciyar masoya, tini zuciyata ta babbake da sonki abar tinanina, Ina sonki so marar misaltuwa.

-bazan taba mantawa da wannan ranar ba wadda dare yayi na kasa bacci acikinta, saboda tsabar tinaninki wato ranar da na fara ganin ki nayi kewarki.

-idan har ba kya jin irin yadda nake ji a kanki a yanzu to tabbas na san zaki ji irin hakan bayan na mace.

-ke kadaice nake gani kullun a cikin baccina, kece abar begena kuma kece wadda nake tsammanin samun farin ciki da nake fata, Ina sonki.

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top