KALAMAN SOYAYYA MASU RATSA ZUCIYA
💝💞💕😈💔😆💙😋💚😌💗😊💜😎
-Ke kamar hasken wata ki ke mai hasken da ke haskeidaniya, haka kuma kalamanki tamkar siga suke ma’abocin zaki, tabbas kin yi kama dakanki hakan ya sanya na ji ina son ki.
💜😎💜
-Alokacin da kika ji kina son wani, to yi maza ki adana sunan shi a cikin ɗaya daga cikin kogunan dake a cikin zuciyarki, domin kuwa ita zuciya takan iya raunata a koda wane lokaci amma shi kogon zuciya ya kan kasance tareda ajiyar da aka yi a cikin shi har abada, Inafatan zan kasance ni ne wanda za ki adana amaɓoya mafi sirrinta soyayya da masoyi, Inason ki.
💓💔💕💖
-Sauda yawan lokaci idanuwana sukan yi kishi dazuciyata, Kin kuwa san mene ne dalili? Saboda a koda yaushe kece abu mafi kusanci da zuciyartawa su kuma idanuwa kin kasance mai yin nesa da su, Ina son ki sosai da zuciya ɗaya.
💔💓😅💝😐💙😋💘😊
-Na kasance ma’abocin soyayya zuciyatama ta gaskata hakan, lokaci na shuɗewa soyayyar ki na ƙaruwa a cikin zuciyata, a lokacin da ki ke cikin farin ciki kyakkyawar fuskar ki na bayyanar da murmushi mai taushi da tausasa zuciyarma’abocin kallonta, kece wadda na ke so a cikin zuciyata babu wata da zata iya canja matsayin ki a wajena, Ina ƙaunar ki.
-SO tamkar rayuwane, ba ko yaushe yake zamowa abu mai sauki ba haka kuma ba a koda yaushe yake wanzar da farin ciki ba, to amma mene ne zai sa matsawar muna raye darai da lafiya za mu yanke alakar soyayya a tsakaninmu, Har zuwa yau babu kamar ki a cikin zuciyata domin kuwa jin muryar ki a kullum na rubanya adadin soyayyar da na ke yi mikia cikin ko wane dare ko safiya, karda ki rabu da ni dan Allah, domin hakan zai iya sanyawa na zamo mutum mai rauni arayuwata
-SO tamkar kurbar ruwan shayi yake mai tsananin zafi, a karon farko zaka kasance cikin shaukin begen shi wanda daga bisani kuma zai ƙona maka harshe na tsawan lokacin da zaka shafe kana yin jinyar shi.
-Soyayyar da na ke yi miki tamkar tafiyace mai nisa da na fara yinta wadda bata da lokacin yankewa har abada Na san burina zai cika matsawar ina tare da ke domin kuwa dukkanin burina yanzu bai wuce na samun ki a matsayin matata uwar ‘ya’yana ba, Ina son ki fiyeda gwal ko kuɗi.
KALAMAN SOYAYYA MASU SANYA MASOYA MURMUSHI GUDA (9)
-Karda ki fadawa kowa kalaman sirrin bude soyayya da kawancen dake tsakanin mu, domin kuwa a dukkan lokacin da kika furta wadannan kalaman sirri ga wani wato “INA SONKA” hakan na nuni da cewa zai yi amfani dashi wajen bude mana akwatin soyayyar mu tasirri wanda hakan zai bashi damar yi mana gagarumar sata har ya yi sanadiyar raba ni da ke har abada, Ina son ki.
Kalaman Soyayya masu dadi da Sanyaya Zuciyar Masoya 2022
-Na yi shiri tare da niyar turo miki da dikkanin soyayyata amma sai dai wanda zan turo da sakon nawa gare ki ta hannun shi ya bayyana hakana matsayin wani babban abu da zai gagari bil’adama ɗauka, amma karda ki damu zanzo nan bada dadewaba domin ki tabbatar da abun da na ke faɗa gaskiyane dama an ce zuwa da kai ya fi saƙo, Ki huta lafiya farin cikin zuciyata, Ina son ki.