KALAMAN SOYAYYA MASU SANYA MASOYA MURMUSHI GUDA (9)

KALAMAN SOYAYYA MASU SANYA MASOYA MURMUSHI GUDA (9)

💓💗😉💚😌💑😃💜😎💕😇

-Ance so aljannar duniya ban fahimci hakaba sai da na kurbi zakin ɗanɗanon zumar soyayyarki sai kawai naji nayi suman zaune uhmmm ban ankara ba sai na tsinci kaina a sararin samaniya muna shawagi cikin duniyar masoya ina baki furennin lovayya.

-bazanyi nadama ko dana sanin zaben ki da nayi a matsayin masoyiyata ba, saboda kece zuciyata ta zaba kece wacce raina ya aminta da ita, hakika burin zuciyata a gareki shine ki zama uwar ƴaƴana mukasancea tare har fitar numfashin mu.

-Zanso ace nafi kowa matsayi a zuciyarki domin ina da yaƙinin nafi kowa ƙaunar ki shiyasa nace a kaf faɗin duniyar masoya babu tamkarki a fagen iya sarrafa zuciya da daddaɗan kalaman soyayya tabbas nayi dace da na kasance sarkin mulkin zuciyarki.

-Ina son dukkan taurarin da suke bisan sama, amma baza’a haɗa son da na ke yi musu da kuma na wadda ta ke a cikin idanuwan ki ba, ina son ki.

-Lokaci yana nan zuwa da zaki mallakawa wani zuciyarki, ina mai yin kira a gare ki da ki tabbatar da cewa kin mallakawawanda ba zai raunata zuciyar ki ta hanyar yaudara kocin amana ba, saboda ita zuciya ɗayace babu wadda zaki daukoki sauya a lokacin da bakin ciki da damuwa suka mamaye zuciyar ta ki.

-Yanzu haka ina cikin farin ciki, shin kin kuwa san menene dalili? Hmm saboda na kasance mai sa’a, kin kuwa santayaya, Saboda Allah ya na so na, kin kuwa san me ya sanya na ce haka, Saboda ya ba ni wata babbar kyauta, kin kuwasan mene ne, Ba komai ba ne ba face KE masoyiyata, inason ki.

-A koda yaushe lokaci tashi yake yi tamkar tsuntsu, amma ita soyayyar mu kullum ginuwa ta ke tare da kara samun wajen zama a cikin zuciyoyin mu karda ki manta da ni ki kasance mai yin tinani na kamar yadda nima na kasance a ko da yaushe.

-Abun da na ke ji a dangane da ke gaskiya ne kema nasan kin san da haka cewa ina son ki, a duk lokacin da kika barni ba zan iya motsawa ko da nan da can ba, wannan shi ne abunda zai faru da ni a duk lokacin da na rasa ki.

-SO tamkar wata sarkar zinari ce da ta ɗaure zuciyoyin mu a waje guda, a dukkan lokacin da kika tsinka waccan sarka tofa ki tabbatar da cewa tamkar kin kore farin cikine daga cikin zuciya ta.

-Masoyina ina son ka, me ya sanya ka ke yin kokwanto a bisa kalmar so da na furta a gare ka, Tabbas kaine mutum nafarko da haduwa da shi ya kore min bakin ciki, ya wanzar da farin ciki a zuciya ta ya yalwata murmushi a saman fuska ta hakane dalilin da ya sanya na ke kiran ka da SADAUKI.  kayi nasara ka yi nasarar jan ra’ayin soyayya ta a kan ka kaine namallakawa linzamin zuciyata, kaine mutum na farko da na tabafurtawa kalmar SO kuma a yanzuma zan kara mai maitawa a gare ka ina son ka. Ka amince mu yi tsaftatacciyar soyayya. Sai yanzu na gano cewa a duniya babu abun da ya kai samun masoyi daɗi, a duk lokacinda na rasaka ban san halin da zan shigaba, daga karshe ina mai sanar da kai cewa buri na yanzu bai wuce na ganin ranar da zaka zamo ango ni kuma na zamo mata a gare kaba, ina alfahari da kai a duk inda na kasance, ka huta lafiya daga mai son ganin farin cikin ka a koda yaushe.

KALAMAN SOYAYYA MASU SANYA MASOYA MURMUSHI GUDA (9)

-Soyayyata da ke ba ta mutuwa kuma ba ta tsoran mutuwa ko daza a yi mana kwace, ko da za mu mutu ko za mu lalace to soyayyar mu za ta kasance a raye na bayar da zuciyata na karbi taki na kamu da sonki. Ki tallafi rayuwata da ta tsunduma a kan tsananin soyayyarki, ki tausayawa zuciyar da tashagala a kan tsananin soyayyarki ka da rintsi ko zugar mahassada ya sa ki guje ni ko kuma ki rage son da kike min, sonki yana dankare a zuciyata kamar yadda kwakwalwa ke dankare a kan ɗan adam da a ce zan samu ikon fito miki da shi da na yi domin ki kara gazgata tsananin kaunar da nake miki.

Kalaman Soyayya Masu Sanyaya Zuciyar da Nishadan Tarwa

-Ina ma a ce na kasance da ke a duk bugun numfashina, kaunar kice take kara tasiri a ruhina, babban burina na ga bayyanar fitar murmushinki a kan wannan kyakykyawar, fuskarki ya kuma zamana ni ne sanadin hakan. 

-Tambarin sarautar girma da ɗaukaka nake dokowa zuwaga sarauniyata mai mulkin birnin zuciyata haƙaƙi kece gimbiyata wacce na damƙa farin ciki na da walwalata a karkashin inuwar kulawarki.

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top