KALAMAN SOYAYYA MASU SANYA NISHAƊI
-Na yarda na amince bamai rabamu in ba mutuwa ba Shiru na baya nufin na mantaki, kobani ki kulawa, saboda ko yaushe a cikin zuciya ta Kece kullum kike kusa da ita, sai da saife Daga lokacin da zuciyata ta kamu da kaunarka bansake fadawa cikin yanayi na damuwa ba.
-Samuwar ki a cikin rayuwata ya samar da gagarumin canji ga ‘karuwar farin ciki na, tahanyar sauraren muryarki da kuma kasantuwata a tare da ke cikin rayuwarki mai tsari, Duk wani abu da zan furta yau a gare ki ba zai wuce, ina Son ki ba, ke ce tauraruwar da hasken ta yake haskaka birnin zuciyata, sannankuma kina ɗaya daga cikin mutanen da ba zan taɓa mantawa da su ba har abada a rayuwata, ki huta lafiya.
-Inason dukan taurarin da suke sararin samaniya sai dai su ba komai bane idan aka kwattan tasu da yanda kike, idanun ki Kalmomi 3 sukan sa zuciyata ta buga cikin sauri,
-kalmomi3 sukan sa kafata ta girgiza, kalmomi 3 sukan sa kai na ya girgiza, wannan kalmomi sune: Ina Son Ki.
-Da akwai miliyoyin furanni a cikin lambun masoya a wannan duniya, Da a ce zan tsunko kowanne fure na baki shi a hannunki, hakan bai isa ya bayyanar da adadin yadda nake son ki ba. Ke ce murmushi na, kuma ke ce farin ciki na, Ina Son Ki.
-Karki damu, bar kuka, share hawayen ki, ni dake ba mai rabawa.
-Kowata safiya na kan tashi cikin farin ciki saboda nasan zan ganki, Masoyiyata bansan dadin soyayyaba sai da muka hadu, karin Sanin daɗin sai munyi aure.
-muzauna guri ɗaya, inayima hidima wadda na tanada miki, ina sonki, kiyi barci mai daɗi kafin mufara a tare.
-Ke tamkar gishiri ce a cikin rayuwa ta, idan na rasa ki zan yi rayuwa ne da babu armashi a cikinta, Ki huta Lafiya.
-Nagina soyayyarki bisa yarda da amincewar zuciyata wacce bazata taba gushewa ba Zuciyata kamar kwalba ce, sonki kuma kamar ruwane wanda ya daskare a cikin ta, cireshi sai dai a fasa kwalbar, Ina son ki zamo mallakina a cikin mafarkina da kuma a zahiri, ki zamanto cikin hirata da sauran dukka zantukan bakina, faruwar hakan zai inganta farin cikin zuciya ta.
-Soyayya shine a duk lokacin da ka kalli cikin idunuwar wani kaga dukkan abin da ka bukata, kamar yadda na nagani a idanun ki, ina sonki.
-Alokacin da na samu soyayyarki sai na ji tamkar ni ne na fi kowa sa’a a duniya.
-Adukkan sanda na rintse idanuwa na sai na hango ni tare da ke muna tafiya a bisa gajimare, Idan na kwanta bacci sai na yi mafarkin mun zama mata da miji.
-Tsuntsaye na buƙatar fukafukai domin tashi, kifi na buƙatar ruwa domin ya yi rayuwa, ni kuma ina buƙatarki domin na yi rayuwar farin ciki, Ina son ki masoyiyata.
-Ba zantaba barin ki ba, saboda ke ce rayuwata, Soyayyarmu tamkar babban lambune mafi girma a duniya, Ina sonki.