KALAMAN SOYAYYA MAZA DA MATA

KALAMAN SOYAYYA MAZA DA MATA

Zuwa ga Maza

-Tsuntsaye na bu’katar fukafukai domin tashi, kifi na bukatar ruwa domin ya yi rayuwa, ni kuma ina bukatarka domin nayi rayuwar farin-ciki. Ina son ka masoyi na!

-Ina son jinka a kusa da ni, ta yadda numfashi na da naka zasu gauraya, ta yadda zan ke juyo sautin bugun zuciyoyinmu na fita a tare. Mu kasance a tare har abada, InaSon Ka!

-A kullum na kwanta bacci, na kan yi mafarkin ka zama uban ‘ya’ya na, ni kuma na zama mata a gare ka, Sai dai nasan iya mafarki ba zai wadatar da ni ba a bisa kulawar da nake tinanin samu daga wajenka, A saboda haka nake fatan mafarki na ya zama gaskiya watarana, Ina Son Ka!

-Ina Son Ka, zan kuma ci-gaba da sonka tun daga futowar rana har izuwa faduwarta a cikin kowace rana har abada Kahuta Lafiya.

Zuwa ga Mata

A lokacin da na samu soyayyarki sai na ji tamkar ni ne na fikowa sa’a a duniya, A dukkan sanda na rintse idanuwa nasai na hango ni tare da ke muna tafiya a bisa gajimare Idanna kwanta bacci sai na yi mafarkin mun zama mata damiji. Ina sonki, tare da son kasancewa a tare da ke har, abada Ki huta Lafiya.

-Sama cike take da taurari masu hasken da ke haske duniyaa cikin kowanne dare, Amma haske mafi haskaka fuska da yaye duhun zuciya, na gan shi ne a cikin, idanuwanki Ki Kula Min Da Kanki. Ina Son ki.

-Furanni na furta kalmomin yabo a kanki a dukkan lokacin dana shiga lambu mai d’auke da ‘korama gami da korayen ciyayi da bishiyu masu dauke da tsintsaye, Sukan rera baitukan yabo a gare ki, cikin harshen da zuciya ce kawaike iya fahimtarsa. Ina Son Ki.

-A mafarki da kuma a cikin soyayya babu abun da ba zai iyafaruwa ba, Ina son ki sosai hakan ya sa nake ji tamkar bazan iya rayuwa idan ba tare da ke ba, Ba na fatan rasa ki a rayuwa ta, domin kuwa a dukkan lokacin da na rasa ki na tabbatar da rayuwa ta za ta shiga garari, Ina Son Ki kumaba zan taɓa canjawa a kan hakan ba.

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top