KALAMAN SOYAYYA ZUWA GA ABAR ƘAUNATA
-Idan na saci kallonki, da nufin yi miki kallon so da ƙauna, sai naga kin kalle ni, kin sunkuyar da kai, cikin salo da yanayi na jin kunya, kina mai murmushin so da ƙauna a gare ni. Wannan tattausan kyakkyawan murmushin na so da ƙauna da kike yi a gare ni, yana ƙara inganta shaƙar numfashi da fitar numfashin a gare ni.
-Abu ne mai sauƙi afkawarka a cikin duniyar soyayya. Sai dai, samun wanda zai yi maka masauki da shimfidar fuska saboda Allah, ba don wani abu naka ba, a cikin duniyar ta soyayya, abu ne mai wuya.
-Duk iyakar inda mace ta kai a kyau, in dai har zan tuna da ke, sai kyawonta a gare ni ya rikiɗe izuwa muni! Ke kaɗai idanuwana suke kallo da kyau na haƙiƙa a dukkan ‘yan matan duniya.
Ga Jerin kalaman Soyayya maza da mata
-Aduk lokacin da nake cikin damuwa idan na kalli fuskarki acikin tunanina sai damuwar ta gushe, idan kuwa ina cikin annashuwa sai naita kwaɗayin kema ki kasance acikin haka💘
-Na gamsu, na yarda, kuma na saka araina, kece zaki bani kulawar da zata sanyaya raina har na manta da dukkan ƙunci da damuwa, kuma nayi tattalin kaina, na taimaki kaina, na tsaya da kafafuna💕
-Dukkan wani nau’in baƙin cikinki mallakina ne, kuma ina farin ciki da farin cikinki, bazan iya jure ganinki acikin matsala ba, zan kusanceki koda kuwa baki buƙaci tallafawa ta ba💔
Wasikar soyayya Zuwaga Tauraruwar Zuciyata
-Soyayyarki tayi tasiri matuƙa a gangar jikina, ta mamaye dukkan tunanina, nayi miki alkawarin zan lallaɓaki, zan kwantar miki da hankali alokacin da kika samu rauni Zan jera tafiyata da taki dan shaƙuwarmu, duk da kasancewar nasan al’umma zasu fara faɗar cewa muna kama da juna, Kwatankwacin siffarki, haka nake tsammanin siffata, idan so samu ne, al’umma su kirani da lalataccen maigida, amma tabbas zan rakaki duk inda zakije, zan jure hawa tsani, zan jure gangarar tudu da tsauni in hidimta miki batare da zaɓi ko kokwanto ba Dukkan abinda na mallaka idan kina buƙata zan mallaka miki.
-Tayaya zan guji wadda bata ƙyamata ta, wadda tayi kane kane acikin al’amurana, tana girmamani tare da darajani, bata kushe duk wani tsarina ko ra’ayina, tana matuƙar murna aduk inda aka karramani, kuma tana zubar da hawaye aduk inda aka muzguna mini😭
-Zan kula dake tamkar yadda maharbi yake tattalin ƙibiya ɗayar da ta rage acikin kwarinsa, alokacin da bai samu komai ba🙅
-Kafin hawayenki su taru, zan kwarfe su, kafin su zube, zan tare su, bayan sun zubo zanyi yaƙi da duk wanda yayi sanadiyyar kwararowarsu kowanene 💪💪.
Hirar soyayya masu dadi na 2022
-Tun kafin na san ko ke wace ce, na kamu da so da ƙaunarki’ Shi yasa na ce: “So da ƙaunata a gare ki na halitta ne, ba na dalili ba, “don haka ba za su ƙare ba. Saboda, abin da yake na halitta ba ya ƙarewa, sai dai a mutu da shi. Abin da yake na dalili kuwa ƙarewa yake in dalilan nasa ya ƙare.
-Ni sai da na riga na kamu da So da ƙaunarki daga baya nasan ko ke wace ce.
-Abin da na sani dangane da ke ɗin daga bayan shi ne, kina da hankali da tarbiyya ga ki da ilimi, ga ki da nutsuwa. To sanin kasancewarki mai hankali da tarbiyya, da ilimi gami da nutsuwa ɗin da na yi daga baya ne ya ƙara tabbatar da So da ƙaunata a gare ki.
-So gamon jinine, haqiqa sonki ya zamo jinin jikina! Kinfita daban a cikin mata, duk lokacin da na kallleki, sai naga kamar babu kyakykyawar wace sai ke!