KALAMAN SOYAYYAH MASU RATSA JIKI

KALAMAN SOYAYYAH MASU RATSA JIKI

-Ki kwantar da hankalinki masoyiyata babu wataa zuciyata sai ke kadai.

-Yarda da amincewarki gareni, sune zasu tabbatar da soyayyarki tagaskiya a gareni Farinciki baya dorewa a rayuwa sai tare da bakinciki, dan haka kowane hali nike bazan taɓa mantawa dake ba masoyiyata.

-Nakan raba dare ina mai roqon Allah don nemanbiyan buqata, ko kinsan kece abu na farko danike roqon samu.

-Yanayin sanyi kan sa mutum ya takura, tare da lulluɓa da qaton mayafi amma ni duk sanyin da ake idan na tunaki sai naji tamkar yanayin zafi.

-Kamar yadda kowacce bishiya kanyi rassa a, sama kuma tayi saiwa a qasa, haka sonki ya mamaye dukkan jikina, idan na kalleki sai nayi farinciki, idan naji tattausan muryarki, sai nishadi da walwala tare da annashuwa gami da farin ciki sumamaye zuciyata.

-Abun da na ke ji a dangane da ke gaskiya ne kema na san kin san da haka cewa ina son ki, a duk lokacin da kika bar ni ba zan iya motsawa ko da nan da can ba, wannan shi ne abun da zai faru da ni a duk lokacin da na rasa ki.

-SO tamkar wata sarkar zinari ce da ta ɗaure zuciyoyin mu a waje guda, a dukkan lokacin da kika tsinka waccan sarka tofa ki tabbatar da cewa tamkar kin kore farin ciki ne daga cikin zuciyata.

ina son ki, me ya sanya ki ke yin kokwanto a bisa kalmar so da na furta a gare ki?

Tabbas kece mace ta farko da haduwata dake yakore min bakin ciki, ya wanzar da farin ciki a zuciyata ya yalwata murmushi a saman fuska ta hakane dalilin da ya sanya na ke kiran ki da, SARAUNIYA ta, ke yi nasarar jan ra’ayin soyayya ta a kan ki kece na mallakawa linzamin zuciyata, kece mace ta farko da na taɓa furtawa kalmar SO kuma a yanzu ma zan kara mai-maitawa a gare ki ina son ki.

-Ki amince mu yi tsaftatacciyar soyayya, Sai yanzu nagano cewa a duniya babu abun da ya kai samun masoyi daɗi, a duk lokacin da na rasaki bansan halin da zan shigaba, daga karshe ina mai sanar da ke  cewa buri na yanzu bai wuce na ganin ranar da zaki zamo amarya ni kuma na zamo ango  a gari ki ba, ina alfahari da ke a duk inda nakasance, ki huta lafiya daga mai son ganin farincikin ki a koda yaushe.

-Babban burina naga bayyanar fitar murmushi akan wannan kyakkyawar fuskar taki,ya kuma zama nine sanadin hakan.

-banason Allah yakawo lokacin da zakiyi fushi dani sosai,domin kaina bazai iya daukaba.

-Na dade ina kallon taurarin samaniya yayin da naga wacce tafi kowacce haske, saina naga bakowa bace nike ganiba sai ke masoyiyata, So gamon jinine haqiqa sonki ya zamo jinin jikina.

-Kinfita daban a cikin mata, duk lokacin da na kalleki sai naga kamar babu kyakykyawar mace saike.

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top