SAKONNIN KALAMAN SOYAYYA MASU DADI

SAKONNIN KALAMAN SOYAYYA MASU DADI

-burin kowane masoyi yasami abokiyar rayuwa ta gari, a kullum ina yiwa Allah godiya da ya bani nagartacciyar mace “irin ki”
-ina son jinki a kusa dani ta yadda numfashi Na da naki zasu gauraya ta yadda zan ji juyo sautin bugun zuciyoyinmu Na fita a tare, mu kasance a tare har abada, ina son ki.
-Akan kauna Na manta kaina masoyiyata nake tunawa.

-Ina fatan kina lafiya matata, ina nan zaune cikin gida amma zuciyata tana tare da ke, kece kawai nake gani naji sanyi a jikina,ina nan ina jiran dawowarki gida lafiya “ina son ki” ki kulamin da kanki.
-A yayinda naji muryarki nakan manta da duk wata hayaniyar da kunnuwa Na suka saurara a tsawon yini guda, kalaman ki sukan natsar da zuciyata inji tamkar bata taba shiga wata damuwa ba kece muradina.
-Ina son ki zamo mallakina acikin mafarkina da kuma a zahiri, ki zamanto cikin hirata da sauran dukka zantukan bakina, faruwar hakan zai inganta farin cikin zuciyata.
-Babu wani abinci da yake yimin daɗi abakina matuƙar bake kika girka shi ba, ina nan tafe izuwa gare ki da shirin zuwa cin abincin ki mai daɗi, ki kulamin da kanki.
-zuciya kalma ce ta musamman don soyayya, soyayya kalma ce ta musamman don kulawa, kulawa ta musamman ce don ke, ke ta musamman ce agareni.
-masoyiyata ina matuƙar alfahari dake saboda nayi dace da mace ta gari mai addini da kuma tsoron ubangiji mahalicci, ina godiya ga Allah da ya bani ke “ina sonki”
-mace mai natsuwa,mai hankalin,mai tunani,mai tsafta,mai addini,mai alkunya,mai ladabi,mai biyayya, duk ke daya masoyiyata “ina sonki” my love.
Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top