SAKONNIN SOYAYYA GUDA BAKWAI DAKE SANYA MASOYA MURMUSHI
(1)-Inason dukkan taurarin da suke bisan sama amma ba za’a hada son da na ke yi musu da kuma na wadda ta ke a cikin idanuwan ki ba ina sonki.
(2)-Lokaci yana nan zuwa da zaki mallakawa wani zuciyarki, ina mai yin kira a gare ki da ki tabbatar da cewa kin mallakawa wanda ba zai raunata zuciyar ki ta hanyar yaudara ko cin amana ba, saboda ita zuciya É—aya ce babu wadda zaki dauko ki sauya a lokacin da bakin ciki da damuwa suka mamaye zuciyar ta ki.
(3)-Yanzu haka ina cikin farin ciki, shin kin kuwa san minene dalili? Hmm saboda na kasance mai sa’a, kin kuwa san tayaya? Saboda Allah yana sona, kin kuwa san me ya sanya na ce haka Saboda ya ba ni wata babbar kyauta, kin kuwa san mene ne? Ba komai ba ne ba face KE, masoyiyata ina son ki.
(4)-A koda yaushe lokaci tashi yake yi tamkar tsuntsu amma ita soyayyar mu kullum ginuwa take tare da kara samun wajen zama a cikin zuciyoyin mu karda ki manta da ni ki kasance mai yin tinani na kamar yadda nima na kasance a koda yaushe.
(5)-Abun da na ke ji a dangane da ke gaskiya ne kema na san kin san da haka cewa ina son, ki a duk lokacin da kika bar ni ba zan iya motsawa koda nan da can ba, wannan shi ne abun da zai faru dani a duk lokacin da na rasa ki.
(6)-SO tamkar wata sarkar zinari ce da ta É—aure zuciyoyinmu a waje guda, a dukkan lokacin da kika tsinka waccan sarka tofa ki tabbatar da cewa tamkar kin kore farin ciki ne daga cikin zuciyata.
(7)-ina son ki, me ya sanya ki ke yin kokwanto a bisa kalmar so da na furta a gareki? Tabbaskece mace ta farko da haduwa dake yakore min bakin ciki, ya wanzar da farin ciki a zuciyata ya yalwata murmushi a saman fuskata hakane dalilin da ya sanya na ke kiran ki da Habibiyata ina son ki.