Zafafan Kalaman Soyayya Domin Masoya Maza Da Mata

Zafafan Kalaman Soyayya Domin Masoya Maza Da Mata

 Zuwa ga Mata

-Son Ki ya mamaye dikan zuciyata. Ina
kallon ki ne tamkar tauraruwar nan da ta
yi wa saura nisa. Ki huta lafiya,
-Kalmomin da a kowane lokaci nake farin-
cikin furta su gare ki su ne….. Kodan na
san tini kin daÉ—e da sanin adadin yadda
nake son Ki, nake kuma ƙaunar Ki sai dai
kawai na ce bani da kamar KI. Burina a
kullum bai wuce na ganin na mallake ki ba
har abada,
-Na kan ji wani abu a cikin zuciyata, ba
komai bane face fitila wadda ke kunnuwa
a dukkan lokacin da na sanya idanuwana
a cikin naki. Ina son Ki fiye da yadda
alamun hakan ke bayyana a saman
fuskata. Ki huta lafiya.
-Kina daga cikin mutanen da ba zan taɓa
mantawa da su ba a rayuwata. Kin zamo
cikin tinanina. Bana fatan zuwan wani abu
da zai zamo silar rabuwarmu, ko da a ce
mutuwa ce. Ina Son Ki.
-A kullum na kan kwanta da tinaninki, na
kuma farka a cikin mafarkina, na gan ki
zaune kusa da ni, a cikin wani lambu
ma’abocin tsintsaye da furanni. Tabbas a
lokacin murmushinki ya fi komai jan
hankalina, muryarki kuma ke samar da
nutsuwata. Ki Huta Lafiya.

Zuwa ga Maza

-A dukkan lokacin da ka furta baka so na,
babu inda ya fi dacewa da na ci gaba da
rayuwa a cikinsa face kabari, domin kuwa
na san daga ranar duniya za ta zamo
wajen zubar hawayena. Ina Son Ka.
-Rayuwata ta kasance rataye cikin tarkon
soyayyarka, ka É—ana kuma ya kama ni. A
dukkan lokacin da na kalli ƙwayar
idanuwanka, na kan ji wani shauƙi mara
misaltuwa. Ina Son Ka.
-Ina cikin kewarka, ina cike da É—aukin son
ganin Ka, a cikin kowace rana son ka na
lunkuwa a cikin zuciyata, fiye da yadda
fatar bakina za ta iya furta hakan. Ka huta
lafiya.
-Abu mafi tsanani wajen sanya zuciya a
damuwa shi ne, ka samu wanda kake so
shi kuma a lokacin ya faÉ—a a son wata.
Bana fatan hakan ya kasance a tsakanina
da kai. Ina Son Ka! Ina Son Ka!! Ina Son
Ka!!! Masoyina.
Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top