ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYA MASU SAKA SHAUKI DA ƘARA ƘARFIN SOYAYYA

ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYA MASU SAKA SHAUKI DA ƘARA ƘARFIN SOYAYYA

 -Yaboda Jinjina Zai tabbata gareki ɗiyar kirki da aminchi duk wata fata na Alkhairi Dole nai miki shi kin zaburar da Zuciya Ta daga dogon suma na rashin irinki a rayuwata Zuciyata Ta Aminta Da Kalaman Ki Domin suna saka ni farin ciki, HubbyNa kece Abu mafi Ɗanɗanon Zaƙi mai canja tinani acikin rayuwata tankaden da nayi da kuma Reraya, Naga Ribar Shi Akanki, Habibiyata Ina ƙaunar ki da Zuciyata da kuma, Raina Zan Cigaba da ƙaunar ki Har Zuwa Ranar Dana Daina Numfashi, Sahibata Ina Son Ki, Soyayyar ki ta rufemin idanu Bana Son Naji ko a Mafarki Labarin Soyayyar wata ɗiya Mace Sai naki HubbyNa, Samun ki Sa’ace gareni Babba Matata, Daga ƙarshe ina Fatan Sahibar Ruhina Tana cikin ƙoshin Lafiya. Sannan Ina Fatankina Cikin Farin Ciki. Ina ƙaunar Ki.

 -haƙiƙa kece mace ta farko wacce na yi gamo da ita karon farko, bantaɓa zato ko tsammanin za’ayi wata ƴa mace wacce zata sace min dukkanin ruhina mafi ƙanƙantar lokaci ba sai ke, amma sai gashi ba tsammani nayi kicibus da kyakkyawar fuskar da na kasa ɗauke wa kallo, Haƙiƙa kyauwun ki yakai ayi misali dashi, kinsha gaban duk mai tinani, zuciyar ki Kyakkyawace, tafiyar ki mai tsari ne, Rayuwar ki abar kallo da koyi ce, lallai nayo matukar Sa’ar samun mace kamarki a cikin rayuwata Muradina, Annuri na, Kuma Shalelen Zuciyata.

 -Tambarinsarautar girma da ɗaukaka nake dokowa zuwaga sarauniyata mai mulkin birnin zuciyata haƙaƙi kece gimbiyata wacce na damƙa farin ciki na da walwalata a karkashin inuwar kulawarki.

-Ance so aljannar duniya ban fahimci hakaba sai da na kurɓi zakin ɗanɗanon zumar soyayyarki sai kawai naji nayi suman zaune uhmmm ban ankara ba sai na tsinci kaina a sararin samaniya muna shawagi cikin duniyar masoya ina baki furennin lovayya.

 -bazanyinadama ko dana sanin zaben ki da nayi a matsayin masoyiyata ba, saboda kece zuciyata ta zaba kece wacce raina ya aminta da ita, hakika burin zuciyata a gareki shine ki zama uwar ‘ya’yana mukasancea tare har fitar numfashin mu.

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top