Tallafin Karatu Na Kamfanin Shall: Sun Bude Application Na 2022 NNPC/NEPCo National University Scholarship
Kamfanin Shell na nigeria (SNEPCo) a madadin NNPC suna sanar da daliban Nigeria musamman ma mata cewa sun bude Scholarship dinsu, dan haka duk mai bukata sai yayi kokarin nema kafin su rufe.
Abubuwan da ake bukata:
1-Dole sai idan kai dan Nigeria ne
2- Sai ya zama kana Shekara ta biyu ne kuma a Jami’a
3- Sai ya zama kana da CGPA 3.5 mafi karance
4- Sannan sai ya zama babu wani Scholarship da kake amfani dashi na kasa ko kuma na kasa-da-kasa
5- Dole ya zama kana da E-mail da kuma Lambar waya
6- Zaka Shigar da bayanan ka da suka hada da:
Bayyqlannan Abubuwan Da Ake Bukata Domin Cikewa
(a) Pasport wanda yake a Format din JPEG, kuma kar ya haura Kilobytes 200
(b) Admission letter na JAMB ko na Jami’a
(c) Jamb result dinka
(d) O’level dinka ko A’level (OND, NCE)
(e) Letter of Identification daga jihar ka ta asali da take nuna karamar hukumar ka ta asali
(f) Sakamakon jarabawar ka (Transcript) na Level 100 na kakar karatu ta shekarar 2020/2021
Lokacin da za’a rufe:
1- Kowanne dalibi ya tabbata ya tura da bayanan sa daga yau 6 March 2023 zuwa ranar 14 ga watan April, 2023
2- A karshe za’a sanar da bayanan lokacin da za’ayi Jarabawar
3- Domin nema ka dannan wannan link din https://candidate.scholastica.ng/schemes/SNEPCo
Muhimmiyar Sanarwa:
1- Application din kyauta ne (Saidai kudin masu cafe
2- Ka ziyarci wannan shafin https://candidate.scholastica.ng/schemes/SNEPCo domin sanin bayanai akan yadda zaka nemi scholarship din
3- Basa tura kowanne wakili (Agent) wanda zai taimakawa dalibai akan yadda zasuyi applying din
4- Basa karba idan ya zama ba nema kayi ba ta Email ne ka tura masu application din.
5- Duk wanda suka kama ya shigar da bayanai na karya to zasu koreshi a kowanne mataki ne.
6- Domin neman karin bayani saika tura da sako ta nan